Da Yiwuwar LMC Ta Dakatar Da Heartland Daga Gasar NPFL

166

Akwai yiwuwar hukumar dake shirya gasar ajin Premier ta kasarnan wato LMC ta dakatar da kungiyar kwallon kafa ta Heartland dake Owerre daga buga gasar cin kofin ajin Premier ta kasarnan.

LMC din zata dauki wannan hukunci ne biyo bayan kutse da shuwagabannin jam’iyyar PDP sukeyi a kungiyar kwallon kafan ta Heartland.

Inda hukumar ta LMC ta bayyana cewar kutsen baidace ba ya kamata abar hukumar gudanarwar kungiyar tayi aikinta ba a shigo da siyasa ciki ba.

Yanzu dai za a iya cewa buga gasar Premier awajen kungiyar kwallon kafa ta Heartland tana kasa tana dabo kenan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan