NAHCON ta sa ranar da alhazan Najeriya za su fara dawowa

211

Shugaban Sashin Kula da Tashin Alhazai a Hukumar Aikin Haji ta Ƙasa, NAHCON, Injiniya Mohammed Goni, ya ce alhazan Najeriya za su fara dawowa gida Najeriya daga ranar Asabar, 17 ga Agusta bayan kammala aikin Haji na bana a Saudiyya.

Mista Goni ya bayyana haka ne a wani taron tattaunawa da aka yi ranar Alhamis da daddare a Makka.

Ya ce jirgin farko, Flynas Airline, wanda zai taso da ƙarfe 7 na safiyar 17 ga Agusta, zai ɗebo alhazan Legas ne zuwa gida Najeriya.

Ya ƙara da cewa a bisa jadawalin jigilar alhazai da Flynas ya bayar, jirage huɗu na farko za su kwaso alhazan Legas ne, yayinda jirgi na biyar zai kwaso na Kebbi.

Ya yi kira ga alhazai da kada su kwaso jakunkunan hannu da yawa, saboda za su tsaya wajen ganin cewa an yi aiki da dokar da ta hana haka.

“Lokacin da ake ɓatawa wajen tantance alhazan dake da jakunkunan hannu da yawa yana shafar fara tashin jirgi a kan lokaci.

“Da zarar an samu jinkirin tashin wani jirgi, sauran jiragen ma za su yi jinkiri”, Mista Goni ya lura da haka.

Ana sa ran cewa kamfanonin jiragen biyu da suka yi jigilar alhazan za su zama cikin shiri a Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Sarki Abdul’aziz dake Jidda ranar 16 ga Agusta don shirye-shirye fara dawowa Najeriya.

Kamfanonin su ne MaxAir da Flynas, na uku, Medview bai iya yin jigilar ba saboda rashin jirgi.

Mista Goni ya roƙi jami’an Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da su haɗa kai da Hukumar, don tabbatar da cewa alhazai ba su ɗauki jakunkunan hannu da yawa ba.

“Dole jihohi su tashi tsaye wajen hana wannan.

“Dole jami’ai su nuna shugabanci abin misali”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan