A yammacin yau Asabar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars zata kara wasan farko na gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika tsakaninta da kungiyar kwallon kafa ta Asante Kotoko ta kasar Ghana.
Tuni dai wannan kungiyar kwallon kafan ta Asante Kotoko ta iso Kano inda a jiya Juma’a ma tayi atisaye a filin wasa na Sani Abacha da yamma.

Za a fara wannan wasa da misalin karfe 4:00 na yammacin wannan rana ta Asabar a katafaren filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a birnin Kanon Dabo.
Kungiyar kwallon kafa ta Asante Kotoko ta taba lashe wannan gasa sau 2, inda itakuma Kano Pillars bata taba lashe gasar ba amma dai ta taba zuwa wasan kusa dana karshe sau 1.

Shin ko Tao yaya wannan wasa zai kasance tsakanin kungiyoyin kwallon kafan guda biyu?

Turawa Abokai