Gwamna Matawalle ya yi wa matasan Zamfara albishir a saƙonsa na Salla

213

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce za ta samar da kadada 3,000 ta ƙasar noma kuma ta saka Naira Miliyan 100 a fannin aikin gona don jan hankalin matasan jihar zuwa aikin na gona.

Gwamna Bello Matawalle na jihar ya bayyana haka a saƙonsa na Barka da Salla ranar Lahadi.

Ya ce tsarin da za a fito da shi zai samar da ayyuka ya kuma yi maganin aikata laifuka tsakanin matasa.

A cewar Gwamna Matawalle, gwamnati za ta kawo ƙwararru da za su horar da matasa a dabarun noma daban-daban, su kuma ba su gonaki, kayan aikin gona, ingantaccen iri da jari don fara shirin ‘juyin juya hali’ a fannin aikin gona.

“A ƙarshen kowace shekarar noma, gwamnati za ta tabbatar da cewa da akwai kasuwa da za a kai amfanin gonar don siyarwa”, in ji Mista Matawalle.

Game da tsaro, Gwamna Matawalle ya bayyana farin cikinsa bisa yadda kashe-kashe da sauran laifuka ke raguwa, yana mai ƙarawa da cewa gwamnati na yin kyakkyawan tanadi don tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’umma.
Ya gargaɗi masu riƙe da sarautun gargajiya a jihar game da yafe wa wata ƙungiyar ta’addanci mai ‘Yansakai’ da suke yi, wadda gwamnonin Arewa 11 suka haramta, yana mai cewa duk wani basarake da aka kama ba za a saurara masa ba.

Mista Matawalle, wanda kwanan nan ya sauke wani sarki mai daraja ta biyu, kuma Hakimin Maru da Kanoma, ya ce gwamnati ba za ta ƙyale wasu su yi barazana ga ‘yancin wasu ba.

An yi bukukuwan Salla yau lami lafiya a Jihar ta Zamfara, inda aka ga mutane da yawa suna shiga Gusau, babban birnin jihar, ba kamar yadda abin yake a baya ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan