Home / Ilimi / Wata ƙungiya a Canada ta ba Sarki Sanusi muƙami

Wata ƙungiya a Canada ta ba Sarki Sanusi muƙami

Ƙungiyar 1 Million Teachers, 1MT ta naɗa Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a matsayin Shugaban Kwamitinta na Bada Shawara a Najeriya.

An kuma naɗa Sarkin a matsayin mamba na Kwamitin Ƙungiyar 1 Million Parent Organisation, One Million Teachers dake Canada.

1MT wata ƙungiyar kyautata rayuwar al’umma ce dake Canada, wadda ke samar da ilimi mai zurfi ga malamai a al’umomin marasa galihu a duniya.

Shugaban Ƙungiyar ta 1MT, Hakeem Subair, ya siffanta naɗin Sarkin a matsayin wani babban ci gaba, kuma wani abu da zai ƙara musu ƙaimi.

Mista Subair ya ce bisa ƙa’ida, 1MT takan nemi muryoyi masu ƙarfi, don taimaka wa wajen samar ilimi mai nagarta kuma na bai-ɗaya ga kowa da kowa, musamman ga manyan mata da ‘yan mata, da kuma ba tawagar tasu shawara.

“Saboda haka, tare da matuƙar jin daɗi, muna yi wa Mai Martaba, Muhammad Sanusi II, CON, Sarkin Kano maraba a matsayin Shugaban Kwamitin Bada Shawara na 1 Million Teachers.

“Da karɓar wannan muƙami, da kuma muƙaminsa na baya bayan nan na mamba a Shirin Muradun Ƙarni, SDG na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya nuna irin jajircewarsa wajen samar da al’umma mai adalci, kuma mun yi matuƙar farin ciki da samun sa”, in ji Mista Subair.

A martaninsa ga wannan muƙamin, Sarkin ya ce: “Ina jira in yi aiki da 1 Million Teachers a ƙoƙarinta na samar da damar samun ilimi mai zurfi ga malamai ga al’ummomi marasa galihu a duniya, musamman a Yankin Sahara na Afirka. A gaskiya, na yi farin ciki sosai game da wannan shiri da irin tasirin da zai iya yi a gaba a ɓangaren ilimi a Najeriya”.

Ƙungiyar dake aiki a ƙasashen Afrika 12 a halin yanzu, 1MT tana aiki da ƙungiyoyin cikin gida da na ƙasashen waje don samar da malamai masu sadaukarwa waɗanda ke zaburar tare da aiki da abokan aikinsu don inganta koyon ilimi na ɗalibai.

About Hassan Hamza

Check Also

Banyakole: Garin Da Mahaifiya Ke Kwanciya Da Mijin ‘Yarta

Yawanci rawar da ƙanwar mahaifiya ke takawa shi ne nuna soyayya tare da shiryar da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *