Hawan Daushe: Hakimai 11 sun bijire wa umarnin Ganduje

143

Hakimai 11 a Jihar Kano sun bijire wa wani umarni da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abudullahi Umar Ganduje ya ba su na cewa su halarci Hawan Daushe a sabbin masarautunsu daban-daban.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Lahadi ne Gwamna Ganduje ya bada umarnin cewa kada wani hakimi ya shigo Kano Hawan Daushe, maimakon haka, duk hakiman su tsaya a sabbin masarautunsu su yi.

Umarnin na Mista Ganduje dai ya saɓa da wanda Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayar da farko, inda ya umarci hakimai 44 na jihar da su shigo Kano don gudanar da Hawan na Daushe ba tare da saɓawa ba.

Sanarwar da Abba Anwar, Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna Ganduje ya fitar, ta ce hakiman da suka faɗo a ƙarƙashin Masarautar Kano ne kaɗai za su halarci Hawan Daushen, sauran hakimai kuma su yi a sabbin masarautunsu daban-daban.

Hakiman da suka bijire wa umarnin na Mista Ganduje suka halarci Hawan Daushen a jiya Litinin su ne Madakin Kano, Yusuf Nabahani, Hakimin Dawakin Tofa; Ɗan Amar, Aliyu Harizimi Umar, Hakimin Doguwa; Dokaji Muhammadu Aliyu, Hakimin Garko; Makama, Sarki Ibrahim, Hakimin Wudil; Sarkin Fulanin Ja’idinawa, Buhari Muhammad, Hakimin Garun Malam da; Barde Idris Bayero, Hakimin Bichi.

Sauran su ne Sarkin Bai, Mukhtar Adnan, Hakimin Ɗanbatta; Yarima Lamido Abubakar, HakiminTakai; Ɗan Isa, Kabiru Hashim, Hakimin Warawa ; Ɗan Madami, Ibrahim Hamza Bayero, Hakimin Ƙiru da; Sarkin Dawaki Mai Tuta, Bello Abubakar, Hakimin Gabasawa.

Wannan dai yana nuna yadda ake ci gaba da samun takun-saƙa tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Masarautar Kano, wani zargi da Gwamna Ganduje yake musantawa koyaushe.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan