Ina son dawowa Najeriya saboda mummunan yanayi da nake ciki a asibitin Indiya- El-Zakzaky

Shugaban Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky, ya yi zargin cewa halin da yake ciki a Asibitin Indiya ya fi muni bisa wanda ya shiga a Najeriya.

Ya ce yana shirye-shiryen dawowa Najeriya don shirin sake asibiti a wata ƙasar.

Mista El-Zakzaky ya bayyana haka ne a wani saƙon murya da ya bazu.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da sahihancin saƙon muryar.

An garzaya da Shugaban na Islamic Movement of Nigeria, IMN, zuwa Indiya ranar Litinin, biyo bayan Izinin yin tafiya da wata Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ba shi.

Tun watan Disamba, 2015 ake tsare da Mista El-Zakzaky da matarsa, Zeenat bayan wani arangama da sojojin Najeriya a Zariya, inda aka kashe a ƙalla ‘yan Shi’a 347.

A saƙon muryar, Mista El-Zakzaky ya zargi Gwamnatin Najeriya da yin ƙafar angulu bisa halin lafiyarsa a Indiya.

Wanda ke magana da Hausa, ya ce halin da yake ciki a asibitin a Indiya ya munana sosai.

A cewarsa, an razanar da Hukumar Gudanarwar Asibitin Medanta da cewa kada su karɓe shi.

“Jami’an asibitin sun karɓe mu hannu biyu-biyu, sun faɗa mana cewa sun ajiye motocin ɗaukar marasa lafiya guda biyu, suka shammaci dandazon mutanen dake wurin, suka bi ta wata hanya, suka ce sun yi haka ne don lafiyarmu.

“Da muka je asibitin, sai aka ajiye mu a ƙarƙashin matsanancin tsaro, fiye da abinda muka shaida a Najeriya. Ɓoyewar da aka yi mana yanzu, ba a yi mana ita a Najeriya ba, fiye da gidan yari.

“Ba kamar yadda muka yi yarjejeniya ba, cewa likitocinmu za su duba yadda za a yi mana aiki. A yanzu, sun canza yarjejeniyar. Saboda haka, sai muka ce ba za mu yadda wasu baƙin likitoci su duba mu ba, ba tare da sa idon amintattun likitocinmu ba”, in ji shi.

A saƙon muryar, Shugaban na IMN ya ce yana son dawowa Najeriya don neman asibitoci masu inganci kuma amintattu tsakanin ƙasashen da suke bada taimako.

“Akwai wasu ƙasashe waɗanda ke bada taimako bisa raɗin kansu waɗanda suka haɗa da Malaysia, Turkiyya”, a kalamansa.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan