Mun shirya tsaf don fara dawo da alhazan Najeriya gida- NAHCON

157

Hukumar Aikin Haji ta Najeriya, NAHCON ta ce ta shirya tsaf don fara dawo da alhazan Najeriya gida daga ranar 17 ga Agusta.

Kwamishinan NAHCON mai Lura Da Aikace-aikace, Saleh Moddibo ya bada wannan tabbaci a wani taron tattaunawa na bayan Arfa da masu ruwa da tsaki a aikin Haji suka halarta a Maka ranar Juma’ar nan.

A cewarsa, an tsara jiragen farko da za su taso ranar 17 ga Agusta su ne MaxAir da Flynas.

Ya ce tuni aka kafa kwamitoci da za su tabbatar da cewa an dawo da alhazan gida Najeriya lami lafiya.

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai na Harkokin Ƙasashen Waje, Muhammed Bulkachuwa, ya yabi NAHCON bisa yadda ta tsara wuraren saukar alhazai da yadda ta ciyar da su a Saudiyya.

Ya bayyana shirin Majalisar Dattijai na fito da yin dokoki da za su inganta yadda ake gudanar da zirga-zirgar aikin Haji.

Da yake sanar da taron tattaunawar aikace-aikacen tawagar likitoci a lokacin aikin Hajin na bana, Shugaban Tawagar Likitocin, Dakta Ibrahim Kana, ya ce likitocin sun yi aiki tuƙuru don tabbatar da lafiyar alhazai.

Amma, ya bada shawarar da a shigo da karɓar kuɗin ganin likita Riyal ɗaya na Saudiyya don hana alhazai yin dandazo don karɓar magunguna kawai.

Mista Kana ya siffanta ɗabi’ar irin waɗannan alhazai a matsayin ɗaya daga cikin ƙalubalen da suke fuskantar kwamitin a wajen gudanar da aikinsa.

Ya roƙi alhazan dake da irin wannan halayya da su daina, yana mai cewa ƙwayoyin magani za su iya zama guba.

Da yake bada gudunmawa, Muhammad Kudu, wani mai ruwa da tsaki a aikin Haji, ya bayyana rashin jin daɗi bisa rashin tsafta da kuma cunkoso da sansanin alhazan Najeriya ya kasance a Muna.

“Wani yanayi da muka samu alhazai 25 zuwa 30 an sa su a tanti ɗaya ba shi ne abu mafi dacewa ba.

“Wasu daga cikin alhazanmu sun bar Muna da cututtuka da ba su nema ba”, in ji Mista Kudu.

Da yake mayar da martani, Shugaban NAHCON, Abdullahi Muhammad, ya danganta rashin tsaftar sansanin Najeriya da yawan alhazai da kuma halayyar ko-in-kula ta wasu alhazai ga muhallin.

Ya yi kira da a ƙara ilmantar da alhazai bisa buƙatar tsaftace tanti-tanti ɗinsu koyaushe.

A cewarsa, Muna, wadda tun asali an tsara ta ne ta ci mutum 950, takan ɗauki mutum miliyan biyu a ranar Arfa da sauran aikace-aikacen addini.

A tasa gudummawar, Alhaji Abdul Hakeem, Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Ogun, ya roƙi alhazai da su ƙyake maƙasudin da ya kai su Saudiyya ya yi jagora a rayuwarsu.

Jakadan Najeriya a Saudiyya, mai ritaya Mai Shari’a Muhammadu Dodo, manya-manyan jami’an NAHCON, masu kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama da malaman addini duk sun halarci taron tattaunawar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan