Home / Gwamnati / Buhari ya koma Abuja

Buhari ya koma Abuja

A ranar Asabar ɗin nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan wata ziyarar aiki ta kwana tara, wadda ta haɗa da yin Salla Babba da ‘yan uwansa da kuma ƙaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa a Jihar Katsina.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa kafin ya bar Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’Adua dake Katsina don zuwa Abuja, Mista Buhari ya hori sojoji da su yi aiki tuƙuru wajen dawo da zaman lafiya a ƙasar nan, musamman a jihohin da mahara suka addaba.

Ya bada umarnin ne lokacin da ya yi wa sojoji jami’ai 15, da sojoji 160 na 17th Army Brigade da Nigerian Air Force 213 Operational Base a Katsina ƙarƙashin “Operation Hadarin Daji” a Filin Jirgin Saman a Katsina.

Yayinda yake mahaifarsa, Daura, Shugaba Buhari ya karɓi baƙuncin Shugaban Guinea Conakry, Farfesa Alpha Conde, inda shugabannin ƙasashen biyu suka yi Sallar Idi a Daura ranar Lahadi.

Mista Conde, wanda ya samu kyakkyawar tarba daga al’ummar Daura, an kuma ba shi wata sarautar gargajiya, an kuma kai shi ya ga Hawan Salla a Fadar Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk.

A cewar NAN, ayyuka raya ƙasa da Shugaba Buhari ya ƙaddamar sun haɗa da hanyoyin ƙauye, inda ya yabi irin ci gaba da ake samu ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Aminu Bello Masari.

Shugaban, wanda ya ƙaddamar da Asibitin Rundunar Sojojin Sama a Daura ranar Alhamis, ya haɗu da waɗanda rikici ya raba da muhallinsu daga ƙananan hukumomi bakwai da mahara suka addaba.

A yayin zamansa a Daura, Shugaban Ƙasar ya karɓi baƙuncin mambobin Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC da shugabancin Majalisar Dokoki ta Ƙasa dana Majalisar Dokokin Jihar Katsina waɗanda suka kai masa ziyarar Salla.

About Hassan Hamza

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *