A yunkurin da kungiyar masu horas wa takeyi na Karrama ta kasar nan kuma reshen jahar Kano ta karrama ‘ya’yanta a wani taro data shirya.
Wannan kungiya tayi hakanne domin kokari da nuna bajinta da ‘ya’yan nata sukayi kuma suke kan yi a kungiyoyin kwallon kafa daban daban a kasar nan harma da kungiyar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekara 20 da wasu ‘ya’yan nata suka tsinci kansu a ciki na masu horas wa.
Kungiyar dai har wasan sada zumunci ta shirya tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da Ma’aikatar Shara’a wato Judiciary F/C, inda Pillars tasami nasara daci 2 da nema.

Haka Shugaban wannan kungiyar Danlami Usman Akawu ya halacci wannan waje har aka gama komai inda ya mika wasu kyaututtukan da hannunsa.
Ga jerin kadan daga cikin wadanda aka karrama:
- An karrama shugaban hukumar kwallon kafa ta jahar Kano kuma mamba a kommetin saukar baki a hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika wato Dr. Rabiu Sharu Inuwa Ahlan.
- Sannan kungiyar ta karrama masu horas wa wato Ibrahim A Musa na Kano Pillars da Usman Abdallah na Enyimba da Rabiu Tata na Jigawa Golden Stars da mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Sharada United da kuma mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Plateau United kuna daya daga cikin masu horas da kungiyar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekara 20 wato Mai Kaba.
- Haka kungiyar ta karrama kungiyar marubuta labarin wasanni ta Kano ganin irin jajircewa da sukeyi wajen zakulo wasanni da wayarwa da mutane kai yadda ya kamata.
- Haka dai kungiyar ta karrama magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da sauransu.
Haka duk wadanda basu sami damar halartar wannan waje ba sun turo wakilansu, inda Muzammil Dalha Yola shine yayi ta kokawa da abin magana wato Mic ganin an kammala abin cikin nasara.