Dangote zai ɗauki ɗaruruwan ɗaliban KUST aiki

216

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano dake Wudil, KUST, ta miƙa sunayen ɗalibai da su ka kammala karatu har 296 ga mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afrika, Alhaji Aliko Dangote don ɗaukar su aiki a rukunin Kamfanonin Dangote.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Shehu Alhaji Musa ya sanar da haka a cikin wata sanarwa ranar Juma’a.

A cewar sanarwar, Dangote, wanda shi ne Jagoran Jami’ar, ya umarci Hukumar Gudanarwar Jami’ar da ta tattara sunayen ɗalibai da su ka kammala karatu da Daraja ta Ɗaya, wato First Class da Daraja ta Biyu, wato Second Class daga 2012 zuwa bana don ba su aiki a kamfanin.

“Don bin umarnin Jagoran Jami’ar, Alhaji Dangote, GCON, mun tattara sunayen ɗalibai da su ka kammala karatu daga dukkan tsangayu daga 2012 zuwa yanzu don miƙawa ga Dangote don ɗaukar su aiki a Rukunin Kamfanonin Dangote”, in ji Shugaban Jami’ar.

“Ɗalibai da su ka kammala da Darajar ta Ɗaya 16 ne, 280 kuma da Daraja ta Biyu”, ya ƙara da haka.

Dangote, wanda shi ne mutum mafi kuɗi a Afrika, haifaffen Jihar Kano, kuma hamshaƙin ɗan kasuwa, ya lashi takobin bada gagarumar gudummawa don kawo ƙarshen talauci da rashin aikin yi a jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan