Barazanar Ɓacewar Ginin Yumɓu Da Tubali A Ƙasar Hausa

314

Babu Shakka Fasali da Tsarin Ginin Kasar Hausa Birni Da Kauye, Gini ne na Yumbu tare da Tubali wanda za ka Ga an Gina Gida mai Dakuna, Soraye tare da Shigifa. A Wasu lokutan ma har da yin bene Na kasa

Gidajen su kan kasance an yi su ne daga yumbu tare da tubali, idan an kammala fasalta gidan akan yi amfani da itace azara wajen yin rufin dakunan Gidan Ko kuma rufa ciyarwar shufci (Musamman Idan Dakunan Shan Kwabo NE) domin kariya daga hasken rana da kuma ruwan damina, sannan kuma akan yi wa gida shafe da makuba tare kuma da yi masa ado

Shekaru aru-aru irin fasali da tsarin ginin kasar Hausa Ke nan, sai kuma ga shi katsam zamani ya riski wannan nau’in gini na Kasa, wanda duk inda ka duba birni da Kauye za ka tarar ginin bulon siminti tare da rufin kwano ne ya ke maye Gurbin ginin Kasa da tubali

Duk da cewa ginin yumbu da tubali na Dadewa bai rushe ba, domin akan samu wanda zai kai tsahon shekaru hamsin a duniya ba tare da ya fadi ba, amma Yanzu abu ne mai wahala ka ga ana yin sababbin gine-gine na kasa, Wanda hakan barazana ce ga bacewar al’adar ginin Bahaushe

Shin Hakan cigaba ne ko ci Baya? Al’ummar Hausawa da za ta taso nan gaba ke nan ba lallai ne ta samu ginin Yumbu da Tubali?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan