Shugaba Buhari Ya Naɗa Sanata Bashir Lado Kwamishina

41


LABARAI

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa tsohon sanatan Kano ta tsakiya wato Sanata Bashir Garba Lado a matsayin kwamishinan a hukumar Kula da ƴan gudun hijira, masu neman mafaka da baƙin haure.

Sanarwar naɗin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa akan yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya sanyawa hannu tare da rabawa manema labarai

Sanarwar ta ƙara da cewa naɗin zai fara nan take.

Saura Waɗanda su ka rabauta da muƙaman sun haɗar da:

Chioma Ejikeme – Bababn Sakataren Hukumar ayyukan ma’aikatun Fansho – Ta canji Sharon Ikeazo

Kashifu Inuwa Abdullahi – Darekta janar na Hukumar NITDA – Ya canji Isa Pantami da aka yi wa Minista.

Bayan haka Buhari ya aika da sunan Adeleke Moronfolu Adewolu majalisar dattawa domin zama kwamishina a Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC).

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan