Babu In Da Aka Haramta Ƙwallon Ƙafa A Addinin Musulunci – Sheikh Ibrahim Khalil

138

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa babu in da aka haramta wasan ƙwallon ƙafa a addinin musulunci, sai dai kawai ana alaƙanta ƙwallon ƙafa da siyasar addini ne.

“Babu in da aka haramta wasan ƙwallon ƙafa a cikin addinin islama, da a ce ina kuɗi to babu shakka zan buɗe ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa guda 100 a faɗin jihar Kano”

Sheikh Ibrahim Khalil ya ce tarihi ya nuna an fara wasan ƙwallon ƙafa fiye da shekaru dubu a duniya, kuma tun a lokacin ƙasashe irin su Misira su ka fara harkar.

Tun da farko shehin malamin ya bayyana hakan ne a filin wasa na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars da ke unguwar sabon gari, a lokacin da ake gudanar da wasan sada zumunci tsakanin masu gabatar da labarin wasanni da kuma masu bugo waya.

“Babu abin da ya ke haɗa da kan matasa fiye da ƙwallon ƙafa, kuma tana samar da zumunci tare da tabbatar da zaman lafiya”

A karshe malamin ya ce a maimakon yara su dinga yawo kwararo-kwararo gwara a samar musu da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa, yadda za’a dinga sayar da su a nahiyar turai.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan