Babu Tabbacin Tsarin Karɓa-Karɓa Zai Yi Tasiri A Jam’iyyar APC A Shekarar 2023 – Gwamna Ganduje

158

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce abu ne mai wahala Jam’iyyar APC ta yi amfani da yarjejeniyar karɓa-karɓa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023
Gwamma Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, a cigaba da bikin kwanaki 100 da fara wa’adin mulkinsa zango na biyu.
Ya ƙara da cewa duk da cewa ba shi ne zai yankewa yadda Jam’iyyar abin da za ta yi ba, amma dai batun zaɓen shugaban ƙasa ana magana akan doron gaskiya da doka.
“Maganar tsarin karɓa-karɓa da gwaman jihar Kaduna ya fara batu akan sa, batu ne tsakanin doron gaskiya tare da tsari. Fasali da tsarin demokaradiyya ya baiwa kowa damar neman kujerar da ya ke muradi, ba tare da yin la’akari daga in da ya fito ko daga wacce kabila ya ke ba. Idan aka bi wannan tsarin to kowa yana da damar jarraba sa’arsa”
“A ɗaya bangaren kuma idan mu ka yi la’akari da zahirin abubuwan da ya ke a ƙasar nan shi ne, Najeriya ƙasa ce mai shiyyoyin siyasa wanda ko a mulkin soji ana amfani da tsarin Kudu da Arewa. Amma a ƙashin gaskiya mutane suna da buƙatar a dama da su daga kowanne tsagi na ƙasar nan walau a Kudu ko Arewa”
Gwamna Ganduje ya kuma ce a wannan yanayin mutane suna batun a samar da mulkin ƙasar nan tsakanin shiyyoyi, amma zahirin maganar shi ne a samar da shugabanci bisa cancanta da dacewa.
A ƙarshe ya ce Jam’iyya ce ke da alhakin zabin salo ko tsarin da ya dace wajen fidda ɗan takara, amma dai siyasa mutane ta ke buƙata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan