Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana shirin mayar da wasu dazuka biyar a jihar zuwa rugage.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar ya sanar da haka ranar Talata a Abuja yayinda yake tattaunawa da manema labarai.
Mista Ganduje ya ce gwamnatinsa ta kafa kwamitin don samar da rugage ga makiyaya a jihar.
Ya ce shirin kafa rugagen zai bunƙasa tattalin arziƙin jihar.
Ya lura da cewa shirin kafa rugagen na da nufin rage zirga-zirgar makiyaya daga Arewa zuwa Kudu da kuma rage rikicin makiyaya da manoma.
“Za mu samar da kayyakin more rayuwa kamar asibiti, asibitin dabbobi, kasuwa, ofishin tsaro da makarantu don makiyaya su yi amfani da su kamar sauran ‘yan Najeriya”, in ji Mista Ganduje.
A cewarsa, shirin kafa Rugagen bai kamata ya zama wani batu na ƙasa ba, kamata ya yi ya zama batun jiha saboda suna rayuwa ne da samu arziƙisu a kowace jiha.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ruɓanya ƙoƙari don tabbatar da cewa manoma sun ci moriyar shirin bada tallafi na haɓɓaka aikin gona a jihar.
[…] Muƙalar Da Ta GabataGanduje zai mayar da wasu dazuka rugage a Kano […]