Gwamnan Rivers Ya Rushe Wani Babban Masallacin Juma’a A Jihar

175

Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, wanda kwanan nan ya bigi ƙirji cewa “jihar ta Kiristoci ce, kuma ba wanda zai iya taɓa ta”, ya fusata a ƙalla Musulmai 10,000 biyo bayan rushe wani masallaci da ake kan ginawa a Trans-Amadi a Fatakwal.

Masallata da suka fusata sun faɗa wa jaridar NewsmakersNG cewa jami’an Hukumar Raya Birane da Tsare-tsare ta Jihar Rivers ne, waɗanda suka zo da jami’an ‘yan sanda ɗauke da makamai suka rushe masallacin ba bisa ka’ida ba, suna masu cewa ba a samu izinin fara ginin ba, duk da izinin fara ginin da aka samo daga Jihar ta Rivers
.
Newsmakers ta ruwaito cewa ginin masallacin, wanda aka fara shi shekaru 10 da suka gabata, an fara rushe shi ne tun a gwamnatin wanda Mista Wike ya gada, Rotimi Amaechi, abinda ya sa aka tafi kotu inda al’ummar Musulmi suka samo wani hukunci da ya ba su umarnin ci gaba da ginin shekaru shida da suka gabata.

Dogaro da hukuncin kotun, sai al’ummar Musulmin suka dawo wajen ginin, sun sa fiye da Naira Miliyan 30 a ginin, kafin jami’an Mista Wike su rushe masallacin, inda Musulmi 10,000 ke taruwa kowace Juma’a don Sallar Juma’a.

Da suke mayar da martani ga wannan al’amari, jagororin al’ummar Musulmi sun yi Alla-wadai da rushe masallacin, suna masu kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ‘yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa da su sa baki su kuma tsawatar wa gwamnan.

Limamin masallacin, Alhaji Haroon Muhammed, ya ce jami’an Hukumar Raye Birane da Tsare-tsare ta Jihar Rivers ne bisa rakiyar ‘yan sanda suka rushe masallacin ranar 20 ga Agusta.

“A Fatakwal gaba ɗaya, wannan shi ne masallacin da yafi kowane ɗaukar jama’a. Musulmi a faɗin duniya gaba ɗaya za su iya ganin abinda ya faru ga masallacin da Gwamnatin Jihar ta bada izinin ginawa. Gwamnatin Jihar Rivers ta ci mana zarafi sau uku, ranar 29 ga watan da ya gabata, sannan sai Alhamis, 15 ga Agusta da 20 ga Agusta ba tare da sanarwa a hukumance ba.

“Yau, an hana mu wajen ibada. Ba ma so mu samu wata matsala da jami’an gwamnati. Muna son duniya ta taimake mu ta roƙi gwamnan don ya canza tunani mu samu wajen ibada saboda Babban Masallacin Trans-Amadi shi kaɗai ne masallacin da yake isar Trans-Amadi.

“Jami’an tsaro, hukumomi, ‘yan sanda, sojoji, ma’aikatan kamfanonin mai da ma’aikatan gwamnati Musulmi nan kaɗai suke da shi wajen yin ibada”, in ji shi.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan