Gwamnatin Tarayya Ta Sa Ranar Da Za Ta Fara Biyan Mafi Ƙarancin Albashi

158

A ranar Litinin ɗin nan ne Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC, Reshen Jihar Ekiti, Kolapo Olatunde ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi da aka daɗe ana jira daga wata mai kamawa.

Mista Olatunde ya bayyana haka a yayin wata tattaunawa da wakilin Ƙungiyar Ƙwadago na Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, ranar Litinin a babban birnin Ekiti, Ado-Ekiti.

“Maganar da nake da ku yanzu a matsayin majiya mai inganci, ba abinda zai hana a fara aiwatar da biyan N30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi daga wata mai kamawa.

“Gwamnati za ta biya sabon mafi ƙarancin albashin a makon farko na Satumba.

“Bayan tarin tattaunawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta NLC a Kano, mun yi maganin duk wani abu da zai iya kawo jinkiri wajen fara biyan.

“A yanzu, muna jiran sakamako”, Mista Olatunde ya bayyana haka

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan