Ambaliyar Ruwa A Kwalejin Barewa Da Ke Zaria

222

An samu wata ambaliyar ruwan sama a yankin unguwar gaskiya da ke ƙaramar hukumar Zaria in da ambaliyar ta shafe shararriyar kwalejin nan ta Barewa.


Ambaliyar ta shafe farfajiyar kwalejin tare kuma da shiga wasu daga cikin azuzuwan ɗaliban makarantar.


Tun da farko dai kwalejin Barewa da ke Zaria an gina ta ne a shekarar 1921 kimanin shekaru 98 da su ka wuce, a ƙarƙashin shugabancin gwamnan ƙasar nan wato Sir Hugh Clifford a zamanin mulkin mallaka.


Tarihi ya nuna ita ce makarantar sakandare guda ɗaya ƙwal a faɗin ƙasar nan da ta samar da firaminista da kuma firimiya tare da shugabannin ƙasa guda 5, da kuma Gwamnoni guda 20, da manyan alƙalai na ƙasar nan guda 3, da Gwamnan Banki guda 2 da kuma ministoci sama da guda 50!

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan