Gwamnan Legas Ya Hana Wasu Ɗaruruwan ‘Yan Arewa Shiga Jihar

72

Gwamnatin Jihar Legas ta tsayar tare da tsare wasu kananan ‘yan kasuwa na Arewacin Najeriya daga shiga jihar sakamakon dandazon shiga jihar da suka yi.

Gwamnatin Jihar Legas ta tabbatar da kama tare da tsare ƙananan ‘yan kasuwar a shafinta na Twitter.

Matasan, waɗanda da yawa ‘yan acaɓa ne, an kama su ne yayinda suke ƙoƙarin shiga Legas.

A ranar Juma’a ne Kwamitin Kar-ta-kwana na Kula da Tsaftar Muhalli da Laifuka na Musamman na Jihar Legas ya tsayar da wata motar ɗaukar kaya da aka loda mata babura 48 da mutane 123 dake zuwa daga Jihar Jigawa”, in ji Gwamnatin Jihar.

“An ƙwace motar ɗaukar kayan, biyo bayan da al’umma suka ankara cewa yadda waɗanda ke cikin motar suka zauna zai iya yin barazana ga tsaro.

“Bayan an tsayar da su, sai aka kai motar da waɗanda ke ciki zuwa ofishin Kwamitin Kar-ta-kwanan dake Oshodi.

“Ɗaya daga cikin waɗanda aka tsare da yake cikin motar, Shu’aibu Haruna, ya ce ya bar Jihar Jigawa ne don ya yi acaɓa a Legas. Ya yi iƙrarin cewa yana da mata ɗaya da ɗa ɗaya, amma ya ce akwai buƙatar ya ruɓanya hanyar samun kuɗinsa don ya iya biya wa iyalin nasa buƙata.

“An yi wannan kamen shiga Legas ɗin ne da ‘yan acaɓa suka yi ba bisa ƙa’ida ba bisa haɗin gwiwar Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na Jihar, Tunji Bello da takwaransa na Sufuri, Dokta Abimbola Oladehinde”, sanarwar ta kara da haka.

Binciken da DAILY NIGERIAN ta yi ya gano cewa babu wata doka da ta hana acaɓa a halin yanzu a Legas.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan