Ibrahim A Musa Ya Tsawaita kwantaraginsa Da Kano Pillars

140

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars wato Ibrahim A Musa ya tsawaita kwantaraginsa da kungiyar a yau.

Inda mai magana da yawun kungiyar kwallon kafan wato Lurwanu Idris Malikawa Garu ya bayyana hakan.

Ya tsawaita kwantaragin ne inda zai fara daga wannan watan da muke ciki har zuwa karshen kakar wasa ta 2019 zuwa 2020.

Sauran wadanda zaici gaba da aiki dasu sun hadar da Ahmad Garba Yaro amatsayin karamin mai horas wa sai Friday Christopher a matsayin mataimakin mai horas wa inda shikuma Muzammil Aliyu shine mai baiwa masu tsaron gida horo da kuma Kabiru Baleria amatsayin team manager na kungiyar kwallon kafan ta Kano Pillars.

Inda suka dauki alkawarin zasuyi aiki tukuru domin ciyar da kungiyar kwallon kafan gaba musamman a sabuwar kakar wasan da za’a fara.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan