An Karrama Gwamna Ganduje A Ƙasa Mai Tsarki

112

Babbar ƙungiyar da ke kula da aikin Hajji da Umra ta Duniya, wato (Hajji And Umra Forum) ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibn Muhammad ta karrama gwamna jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kyautar al’ƙur’ani mai girma na zamani mai ƙunshe da wani yanki na ƙyallen ɗakin Allah (Ka’aba).


Wannan karramawa ta biyo bayan gamsuwa da kyakkyawan shiri da tsarin kula da alhazan jihar Kano da gwamnatin Jihar Kano ta yi.


Da ya ke karɓar kyautar a garin Jidda, mai girma gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje wanda ya samu wakilcin sakataren zartarwa na hukumar kula da jin daɗin alhazan jihar Kano Alhaji Abba Muhammad Ɗambatta, ya yabawa ƙungiyar akan wannan karramawa da ta yi masa, ya kuma ba su tabbacin cigaba da kyautata walwala da kula da jin daɗin alhazan Jihar Kano.


Shi ma a nasa jawabin, shugaban hukumar kula da jin daɗin alhazai ta Jihar Kano, Sheikh Dakta Sale Abdullahi Fakistan, ya taya gwamna Abdullahi Umar Ganduje murna dangane da wannan nasara da ya samu.


Tun da farko a nasa jawabin, shugaban ƙungiyar Sheikh Ibn Muhammad, ya ƙara da cewa ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Kano ta yi wajen kulawa da alhazanta shi ne dalilin da ya sanya su ka zaɓi gwamna Ganduje wajen karrama shi da wannan lambar yabo ta musamman domin nuna masa yadda su ka gamsu da shirinsa da kuma manufar ƙara ƙarfafa masa gwiwar cigaba da kulawa da alhazan Jihar Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan