Antonio Conte Yayi Magana Akan Christian Eriksen

198

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan wato Antonio Conte ya bayyana cewar matukar aka sake bude Kofar musayar ‘yan wasa a nahiyar turai tofa baiga dan wasan dayadace da kungiyar kwallon kafan ta Inter ba kamar Eriksen.

Conte ya kara da cewa matukar Christian Eriksen bai kara rattaba hannu a Tottenham ba to zasu nemeshi.

Kungiyoyin kwallon kafa da dama a nahiyar turai sun nuna sha’awarsu ta daukan Eriksen amma hakansu bai cimma ruwa ba kamar su Real Madrid da Manchester United.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan