Xenophobia: Najeriya Za Ta Dawo Da Jakadanta Na Afirka Ta Kudu Gida

93

Za a dawo da Jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Kabiru Bala gida kowane lokaci daga yanzu don tattaunawa bisa haren-haren ƙin jinin baƙi da ake kai wa ‘yan Najeriya a ƙasar.

Wata majiya a Fadar Shugaban Ƙasa wadda ta bayyana haka ga jaridar The Nation ta ce Najeriya kuma ta ce ba za ta halarci Taron Tattalin Arziƙi na Duniya na Afirka da za a yi a birnin Capetown dake Afrika ta Kudun daga 4 zuwa 6 ga watan Satumba ba sakamakon hare-haren ƙin jinin baƙin da ake ci gaba da kai wa ‘yan Najeriya.

An shirya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne zai wakilci Najeriya a taron.

Dama tuni Jamhoriyar Dimukuraɗiyyar Kwango, Ruwanda da Malawi sun sanar da ƙaurace wa taron.

Shugaba Paul Kagame na Rwanda, Felix Tshisekedi na Jamhoriyar Dimukuraɗiyyar Kwango, DRC da Peter Mutharika na Malawi duk sun bada shawarar janyewa daga taron.

Majiyar ta ce Najeriya ta kuma buƙaci a biya ta cikakkiyar diyya ta waɗanda abin ya shafa.

A cewar majiyar, wannan shi ne sakamakon tattaunawa da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Geoffrey Onyeama bisa yawaitar hare-haren da ake kai wa ‘yan Najeriya a Afrika ta Kudun.

A ranar Talata Mista Onyeam, a wani taron manema labarai da Jakadan Afirka ta Kudu a Najeriya, Bobby Moroe ya jaddada cewa: “Tun a farko, dole mu dubi batun biyan diyya”.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan