Muzahara Ta Jawo Artabu Tsakanin ‘Yan Sanda da ‘Yan Shi’a A Katsina

243

A ranar Talatar nan ne ‘yan sanda da ‘yan ƙungiyar Islamic Movement of Nigeria, IMN, da aka fi sani da Shi’a suka yi taho-mu-gama a yayin Zagayen Tasu’a da ‘yan Shi’ar suka yi a Jihar Katsina, abinda yasa mutane da dama suka samu raunuka.

Mai magana da yawan Ƙungiyar a Katsina, Dokta Abdulkarim Abdulmumin, ya faɗa wa jaridar The Nation ta waya cewa da misalin ƙarfe 8:30 na safe ne ‘yan sanda suka dakatar da Muzhahar kwatsam, wadda suka fara da misalin ƙarfe 7:30 na safe.

A cewarsa, ‘yan sandan sun harba hayaƙi mai sa hawaye, kuma suka yi ta harbin a cikin iska don tarwatsa ‘yan Ƙungiyar.

Ya ce: “Mun raba kanmu ne zuwa gungun daban-daban, kuma muna ta yin tattaki cikin lumana a kan titi a yankin Ƙofar Marusa ta Katsina lokacin da ‘yan sanda suka kutso, an kama ‘yan Ƙungiyarmu da yawa, wasu kuma sun jikkata”.

Amma, lokacin da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Gambo Isah, ya ce dama tuni ‘yan sanda sun yi gargaɗi game da yin kowane irin tattaki a jihar, yana mai jaddada cewa dole Rundunar ta tsaya ta ga cewa an biyayya ga wannan umarni.

Amma, Mista Isah ya ce yayinda Musulmi ke da ‘yanci su yi bikin Ashura a dukkan faɗin ƙasar nan da ma sauran Musulmin duniya, hanin yana aiki ne kawai ga ‘yan haramtacciyar Ƙungiyar IMN.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan