‘Yan Takara 52 Za Su Shiga Zaɓen Gwamnan Bayelsa- INEC

163

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta ce jam’iyyu 52 da ‘yan takarar su sun shirya tsaf don shiga zaɓen gwamnan Bayelsa da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa an kafe wannan sanarwa ne ranar Juma’ar nan a Ofishin INEC dake Yenagoa.

Jam’iyyun su ne Accord, ANRP, ADP, APP and DPP, APGA, BNPP, CAP, PDP, APC, FJPN, FDP, GPN da sauransu.

Wasu daga cikin ‘yan takarar sun haɗa da David Lyon, APC, Sanata Douye Diri, PDP, Azibataram Cameron, ANRP da Helen Okorodas, ACD.

Wilfred Ifogah, Shugaban Sashin Wayar Da Kan Masu Zaɓe Da Watsa Labarai, ya faɗa wa NAN cewa jimillar jam’iyyu 52 sun iya tsayar da ‘yan takara a zaɓen mai zuwa.

A ta bakin Ifogah, ‘yan takarar sun haɗa da maza 46, mata 6.

“To, akwai wasu sauran jam’iyyun, amma waɗannan nan ne suka cika sharuɗɗa kuma suka iya tsayar da ‘yan takara”, ya bayyana haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan