Ba Za Mu Saurarawa Duk Mawaƙin Ko Ɗan Fim Ɗin Da Ya Karya Doka Ba – Afakallah

212

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce ba za ta saurarawa duk wani dan fim ko mawaki ba matukar ya sabawa dokar da ta kafa hukumar ta shekarar 2001.
Hukumar ta furta hakan ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta kara da cewa duk wanda ya fitar da waka ko fim ba tare da lasisi ba za ta dauki “matakin ba sani ba sabo” a kansa.
Sanarwar wadda mai magana da yawun hukumar Ibrahim Adamu K/Nasarawa ya sanya wa hannu, ta ce wannan gargadi ya biyo bayan gurfanar da Naziriu M Ahmad Sarkin Wakar Sarkin Kano da aka yi ne a gaban kotu.
“Babban sakataren hukumar Alhaji Isma’il Na’abba Afakkallah ne ya yi gargadin biyo bayan kamawa tare da gurfanar da Naziru M. Ahmad (SarkinWaka) gaban kotu bisa zargin fitar da kundin wakoki a baya-bayan nan da ya yi ba tare da sahhalewar hukumar ba,” in ji sanarwar.
Sannan ya yi kira ga dukkanin masu shirya fina-finai da mawaka da su tabbatar sun mika wa hukumar ayyukansu domin tantancewa kafin fitar da su kasuwa.
A ranar Laraba ne dai jami’an tsaro suka dira gidan shahararren mawaki Naziru M. Ahmad, wanda aka fi sani da Sarkin Waka.
Sun zarge shi da gudanar da dakin buga wakoki wato studio maras lasisi a cikin gidansa da kuma fitar da kundin waka shi ma maras lasisi.
Har sai a ranar Juma’a ne kuma kotu ta bayar da belinsa bayan ya cika sharuddan da ta gindaya masa.
Makwanni kafin haka, hukumar ta tace fina-finai ta gurfanar da Sanusi Oscar bisa zargin sakin wata waka shi ma ba tare da tantancewar hukumar ba.
Ana ganin wadannan rikice-rikice da ke faruwa tsakanin hukumar da kuma masu shirya fina-finai a jihar Kano ba zai rasa nasaba da rikicin siyasa ba.

Rahoton BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan