An Kama Jami’in Hukumar EFCC Na Bogi A Jihar Legas

60

Wani mutum mai suna Emeka Emmanuel mai shekaru 29 da yake amfani da katin sheda na bogi na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ya shiga komar ‘yan sanda a jihar Legas.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana ya shaidawa manema labarai cewa, mutumin ya dade yana damfarar jama’a da sunan cewa shi jami’i ne na EFCC inda ya ke karbar kudin su da sunan zai samar masu aiki a hukumar.
Ya ce, daya daga cikin wadanda da ya damfara mai suna Olaposi Semiu ya shaida cewa wanda ake zargin ya karbi kudi a wajen sa Naira dubu 51 da sunan zai samar wa dansa aiki a hukumar ta EFCC.
DSP Bala Elkana ya kara da cewa, an sami kayayyakin hada magunguna na jabu da takardun shaida na bogi a gidan wanda ake zargin a yankin Ijaniki a Legas, ya ce za a gurfanar da shi a gaban kotu nan bada jimawa ba da zarar an kammala bincike akansa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan