Abinda Yasa Na Nace Da Zuwa Kotu- Atiku

148

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce ya garzaya kotu ne bisa zaɓen shugaban ƙasa na 2019 don tabbatar da cewa “ƙuri’un ‘yan Najeriya sun yi amfani”.

Mista Abubakar a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja, ya kuma ce ya yi hakan ne don tabbatar da cewa lallai ana yin dimukoraɗiyya a Najeriya.

Ya ce: “Babu wani abu mai kyau da yake zuwa da sauƙi”, kuma ana buƙatar yin aiki tuƙuru a ƙoƙarin raba Najeriya da masu kama-karya.

Ya ƙara da cewa turbar da ya ɗauka don ƙwato nasararsa ita ma ya ɗauke ta ne don dawo da doka da dimukuraɗiyya a Najeriya.

“Wannan babbar ƙasa Najeriya da ta ɗauke ni daga hanyoyin Jada zuwa inda na riƙa siyar da itacen wuta zuwa ƙololuwar matakin da na kai bisa ni’imar Ubangiji a aikin gwamnati, a kamfanonin Najeriya da hidimata wa al’umma tana bi na bashi sosai.

“Idan ban taka rawa daga ɓangarena ba wajen mayar da ita ƙasar da marayu, matasa ‘yan asalin ƙasa da mara galihu za su iya yin yadda na yi har ma su wuce ni ba, to na saɓa wa Mahaliccina.

“Idan ban tabbatar da cewa tsanin da na hau yana nan yadda na ƙasa, na tsakiya da na sama za su iya hawa ba, to ban cika muradina ba.

“Ba kuma kawai ta tabbatar da cewa an yi dimukoraɗiyya a Najeriya ba, amma a ga an yi dimukoraɗiyyar, shin Najeriya da ‘yan Najeriya za su iya jin cewa wannan ƙasa tamu tabbas ƙasa ce inda haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba suka samu gindin zama.

“Saboda wannan ne, da sauran dalilan kishin ƙasa, nake bin wannan turbar shari’ar: don tabbatar da cewa ƙuri’un ‘yan Najeriya sun yi amfani kuma an ƙirga su”, in ji shi.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce waɗanda ba sa so Najeriya ta zama ta cimma muraduntta za su yi amfani da kowace irin dabara don dakushe, kashe guiwa, ruɗar da rikitar da mutane.

Amma, ya ce da taimakon Allah da goyon bayan ‘yan Najeriya, zai tabbatar da cewa Najeriya ta hau turbar dimukoraɗiyya.

“Dole mu dawo a matsayin cibiyar dimukoraɗiyyar Afirka, inda ake bada ‘yancin faɗar albarkacin baki da ‘yanci bayan faɗar albarkacin bakin.

“Dole mu tashi tsaye don tabbatar da adalci a haka ta dukkan hanyoyi, don kada alƙalanmu su riƙa jin tsoron yin aikinsu, kuma su fita daga bi-ta-da-ƙulli, tsoratarwa da cutarwa”, a kalamansa.

Mista Abubakar ya nuna jin daɗi bisa muradi ɗaya da goyon baya da ‘yan Najeriya daga dukkan ɓangarori da kuma kowane ɓangaren al’umma suka ba shi tun daga 21 ga Yuli, 2018, lokacin da ya bayyana aniyarsa ta yin takarar shugaban ƙasa.

Ya ce wannan goyon baya ya ci gaba har 11 ga Satumba, lokacin da Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yanke hukuncinta.

Ya lura da irin fatan alheri da yake samu daga gama-garin ‘yan Najeriya a lungu da saƙo da kuma dukkan yankuna, addinai, da dangi.

“Ina kuma gode wa gwamnoni da aka zaɓa a ƙarƙashin jami’yyata, PDP, da kuma Kwamitin Zartarwa na Ƙasa bisa goyon bayansu mara iyaka a wannan gwagwarmayar shari’a, musamman bayan da aka sanar da cewa za mu ɗaukaka ƙara”, in ji Mista Abubakar.

Ya roƙi dukkan ‘yan Najeriya da su ci gaba da ba shi goyon bayansu a wannan ƙoƙarin neman adalci ta hanyar kotuna.

Ya ƙara da cewa: “Ko abinda za ka iya yi kaɗan ne ko ba ka da abinda za ka iya yi don tabbatar da cewa an yi adalci a Najeriya, kawai ka yi imani cewa hakan za ta faru. Kada mu sake mu raina imanimu da Najeriya”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan