Ya Kamata Gwamnati Ta Ba Turancin Buroka Kulawa- Sarkin Lafiya

165

A ranar Asabar ne Sarkin Lafiya, Alhaji Sidi Bage Muhammad I, ya yi kira da a ba Turancin Buroka (Pidgin English) kulawa don ya zama harshen gwamnati a ƙasar nan, don haɗa kan ‘yan Najeriya ta hanyar magana da shi.

Sarki Muhammad, wanda Alƙalin Kotun Ƙoli ne mai ritaya, ya yi kiran ne a lokacin Taron Ƙasa Karo na 35 na Ƙungiyar Malaman Turanci ta Najeriya, ESAN, bisa haɗin gwiwar Sashin Nazarin Yaruka na Jami’ar Karatu Daga Nesa ta Ƙasa, NOUN a Abuja.

Ya ce lokaci ya yi da za a ba Turancin Buroka kulawa saboda ya ba ‘yan Najeriya damar yin magana a lokacin wahala kamar yadda ake gani a halin yanzu a ƙasar nan.

“Turancin Buroka ya taka rawa sosai saboda ya zama wata hanyar sadarwa a ƙasar nan.

“Wannan ya taimaki ‘yan Najeriya da dama waɗanda ba su iya harshen Turanci sosai ba su yi magana da mutane a matakinmu, kuma ya dunƙule ƙasar nan wuri guda.

“Na faɗa lokacin da muke tattaunawa a Kotun Ɗaukaka Ƙara don ɗaukar matsaya kan wasu batutuwa cewa akwai buƙatar a ba Turancin Buroka kulawa”, in ji Sarki Muhammad.

A cewarsa, ko Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yadda cewa Turancin Buroka zai iya maye gurbin Turanci, kuma saboda haka maganar da aka yi da shi za a iya karɓar su a matsayin hujja.

Ya ce: “An samu wannan muhawara wani lokaci a baya inda za a iya karɓar maganganun da aka yi da Turancin Buroka a matsayin hujja, an sa shi ga fassara da dama, kuma ya fara ne daga matakin Babbar Kotu, har ya zo mana a Kotun Ɗaukaka Ƙara.

“Hukuncin Babbar Kotun shi ne Turancin Buroka ba Turanci ba ne, saboda haka waɗannan maganganu a karan kansu ba za su iya zama hujja ba, ko dai a fassara su da Turanci, wanda shi ne abinda kotun ta ce dole a bar shi ga kotu, kuma zai buƙaci kafa hujjoji da yawa.

“Batun ya zo mana a Kotun Ɗaukaka Ƙara kuma muka zauna da gungun alƙalai don ɗaukar matsaya. Matsayar da muka cimma a Kotun Ɗaukaka Ƙarar shi ne Turancin Buroka Turanci ne, kuma muka ce abinda ke da muhimmanci shi ne yana isar da abinda mai magana ke nufin faɗa.

“Kuma, muka ce mutanen da ake so su fahimci shi suna fahimta, saboda haka Turancin Buroka zai iya tsayawa a matsayin Turanci, kuma za a iya karɓar irin waɗannan maganganu a matsayin hujja.

“Mun yi tunanin cewa waɗanda abin ya shafa za su ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli tunda abu ne na ƙasa don ya zama doka, ba kuma sai an sa shi a wata fassarar ba a gaba ba, amma ba su je Kotun Ƙolin ba.

Farfesa Amina Bashir, wadda ta gabatar da babban jawabi mai taken “Harshe, Adabi, Haɗin Kan Ƙasa Da Ci Gaba Mai Ɗorewa”, ta ce ce ci gaban kowace ƙasa ya dogara ne da al’umma da ƙaunarsu wajen ci gaban ƙasarsu.

Ta ce za a iya cimma wannan ta hanyar harshe wanda ba kawai shi ne ƙarshe ba, amma wata hanya ce ta samun dunƙulewar ƙasa wuri guda da ci gaba mai ɗorewa.

“Harshe yakan zama wata hanyar warware matsala, adabi ya tattara wani curin tunani, ci gaba, dunƙulewar ƙasa wuri guda, tarihi da sana’o’insu na yau da kullum. Duk waɗannan suna nuna inda mutum ya fito, da yadda suka banbanta wajen al’adu.

“Saboda haka, adabi ne ke haska harshe, al’ada, dunƙulewar ƙasa wuri guda, bayar da ma’anar abinda marubuta ke nufi ba tare da canzawa ba, da kuma hoton rayuwa yadda take.

“Adabin Najeriya kamar yadda Chidi Amuta (2005) ya faɗa, shi ne zahirin lamari, hanyar ƙirƙirar tunani, da abubuwa masu kyau cikin taƙaitacciyar da ma’anar zamantakewar harshe ta taƙaita.

“Harshe da adabi a fuskar ci gaba mai ɗorewa ba a raba su. Adabi shi ne jimillar tunaninmu, ta hanyar da harshe ke ba kulawa”, in ji ta.

Malamar jami’ar ta lura da cewa harshe kamar adabi, ba zai iya zama a wajen da ba kowa ba, kuma ba a iya raba su.

Ta ƙara da cewa adabi yana amfani da harshe ta fuskar fasaha wajen haskaka rayuwa, samar da alƙibla ga albarkatunmu, (man fetir, yuraniyum, gwal, azurfa, zinare da sauransu), ilimi, haɗuwa da duniyar waje, tattalin arziƙi da sauransu.

Tun da farko, Farfesa Abdalla Uba Adamu, Shugaban Jami’ar NOUN ya ce taken taron- “Harshen Turanci Da Adabi Don Haɗin Kan Ƙasa Da Ci Gaba Mai Ɗorewa”, ya zo a lokacin da ya dace, duba da yadda abubuwa suke gudana a ƙasar nan.

Farfesa Adamu, wanda ya samu wakilcin Joy Eyisi, Mataimakin Shugaban Jami’ar, ya siffanta harshe a matsayin wata hanyar haɗa kan ƙasa da ci gaba mai ɗorewa.

“Muna dunƙulewar ƙasa wuri guda, muna son ci gaba mai ɗorewa, idan muna son cimma wannan guri, harshe shi ne a sama”, in ji Mista Eyisi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan