Babu Abin Da Shugaba Buhari Ya Tsinanawa Arewacin Ƙasar Nan – Attahiru Bafarawa

234

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa ya caccaki shugaban ƙasa Muhammadu Buhari dangane da salon mulkinsa musamman rawar da yake takawa ga arewacin ƙasar nan.

A hirarsa da sashen Hausa na BBC, Bafarawa ya bayyana rashin tsaro a matsayin babbar matsalar da ƙasar nan ke fuskanta, inda ya bayyana matsalar garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa a matsayin abin da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.

Ya bayyana cewa bai ga wani ci gaba da aka samu ba a ƙasar nan, inda ya ce gara gwamnatin baya da ta yanzu.

Bafarawa ya bayyana cewa “bai taɓa jin shugaban ƙasa ya zauna da gwamnonin arewa ba, domin tattauna matsaloli da kuma mafitar arewa.”

Har ila yau, tsohon gwamnan ya ce ana nuna ɓangaranci wajen gudanar da ayyukan ci gaba a ƙasar.

Ya yi kira ga shugaban ƙasar da ”ya buɗe kunnunwansa domin sauraren shawarwari da za su iya kawo ci gaba a ƙasar nan.

Kalaman na Bafarawa na zuwa ne bayan lashe zaɓe da Shugaba Muhammad Buhari ya yi karo na biyu.

Tun a baya dai, Shugaba Buhari ya bayyana tsaro da yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma tattalin arziki a matsayin abubuwan da ya sa a gaba domin kawo ci gaba a ƙasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan