Gobara Ta Kashe Jarirai 11 A Asibitin Ƙasar Aljeriya

191

A kalla jarirai 11 ne suka mutu yayin da gobara ta tashi da asubahin ranar Talata a wani asibiti a kasar Aljeriya.
Firaiminista Noureddine Bedoui ya bayar da umarnin yin bincike ya kuma tura ministan lafiya zuwa wajen da abin ya faru
Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Captain Nassim Bernaoui, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an ceto mata 107 daga gobarar.
Kyaftin Bernaoui ya kuma ce an ceto wasu ma’aikatan asibitin guda 30.
“Sai dai mun yi bakin cikin rasa jarirai 11 wadanda wasun su suka mutu sakamakon konewa da suka yi wasu kuma saboda hayakin da suka shaka,” in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan