Shugabancin Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah, JIBWIS, da aka fi sani da Izala ta yi kira ga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso da ya nemi afuwa bisa cin mutuncin Sheikh Isa Ibrahim Pantami, Ministan Sadarwa na Najeriya da ‘yan ɗariƙarsa ta Kwankwasiyya suka yi.
Jaridar KANO FOCUS ta Bada rahoton cewa Sheikh Pantami, a ranar Talatar da ta gaba ne magoya bayan Kwankwaso suka ci mutuncin Sheikh Pantami, wanda shahararren malamin addinin Muslunci ne, a Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Malam Aminu Kano, MAKIA, lokacin a kan hanyarsa ta komawa Abuja.
An gano cewa ministan ya zo Kano ne don yin ta’aziyya ga Sha’aban Ibrahim Sharaɗa, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Birnin Kano wanda mahaifinsa ya rasu kwanan nan.
Lokacin da Sheikh Pantami zai hau jirgi, sai ya haɗu da dandazon ‘yan Kwankwasiyya, waɗanda su ma suka je filin jirgin don raka ɗalibai 242 waɗanda Gidauniyar Kwankwasiyya ta ɗauki nauyin karatun digirinsu na biyu zuwa Indiya da Sudan.
An gano cewa lokacin da suka ga Sheikh Pantami, sai wasu ‘yan Kwankwasiyya suka fara ihu: “ba ma yi, ba ma yi’, yayinda wasu suka jawo rigarsa.
Yayinda wannan balahira ke ci gaba da faruwa, kyamara ta ɗauko hoton wani saurayi da aka gan shi yana ƙoƙarin ƙaƙaba wa Sheikh Pantami jar hula- alamar ɗarikar Kwankwasiyya.
Har yanzu dai ministan bai ce komai ba game da wannan balahira da ta faru.
To, sai dai a cikin wata sanarwa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, Shugaban JIBWIS na Ƙasa, ya nuna baƙin ciki bisa wannan abu da ya faru, yana mai cewa ministan, wanda ya tafiyar da mafi yawan lokutansa wajen koyar da karatun Ƙur’ani da fassararsa bai cancanci a yi masa cin zarafin da aka yi masa ba.
Sheikh Lau ya kuma shawarci Kwankwaso, jagoran Kwankwasiyya da ya fito fili ya nemi afuwar Sheikh Pantami da kuma Musulmin Najeriya bisa wannan halayya ta magoya bayansa, yana mai gargaɗin cewa fushin Allah yana jiran duk wanda ke cin mutuncin malaman addinin Musulunci, “waɗanda su ne magada annabawa”.
“Annabinmu mai girma Muhammad (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) ya faɗa mana cewa duk wanda yake ganin tare da girmama malamai waɗanda suka haddace Ƙur’ani Mai Girma, ya girmama tare da ganin girman Allah”. Haka kuma, cin zarafin da aka yi wa Pantami ya saɓa da dokokin Najeriya, saboda a matsayin minista, shi mamba ne na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, FEC”, in ji shi.