Yaudara Ce Ta Sa El-Rufa’i Ya Sa Ɗansa A Firamaren Gwamnati- Shehu Sani

58

Tsohon sanata da ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dokoki ta Ƙasa Zubi na 8, Shehu Sani ya caccaki Gwamna Nasir El-Rufa’i bisa saka ɗansa mai shekaru shida da haihuwa, Abubakar da ya yi a makarantar firamaren gwamnati a jihar.

Mista Sani, lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna ranar Laraba, ya ce Gwamnan ya kashe Miliyan 195 don ɗaga darajar makarantar da ya kai ɗansa.

Tsohon sanatan ya ƙalubalanci Gwamna El-Rufa’i da ya ɗaga darajar sauran makarantu a jihar, idan da ba haka ba, to abinda ya yi zai zama yaudara.

Mista Sani ya ce: “Ba zai yiwu ka kashe Miliyan 195 a wata keɓantacciyar makaranta ba, sannan ka ɗauki ɗanka da kafafen watsa labarai zuwa makarantar, sannan ka yi tunanin ka yi wani abu na daban.

“El-Rufa’i ya tsara wannan abu tsara don samun goyon baya gabanin gwagwarmayar siyasar 2023”, in ji shi.

A cewar tsohon sanatan, dirama ce mara kyau ta Kannywood ko Nollywood da ba a rubuta ta da kyau ba, wadda ake nufin yaudarar al’ummar dake waje da ita, waɗanda ba za su iya sanin mummunan halin da makarantun gwamnati ke ciki ba a jihar.

Ya ce abinda Gwamnan ya yi “shirin siyasa ne na 2023 don kafafen watsa labarai da mutanen dake zaune a wajen Kaduna saboda waɗanda ke zaune a nan sun san yadda makarantun gwamnati suke.

Mista Sani ya ƙara da cewa: “Ba wai don ina da bambancin siyasa da shi ba ne, amma duk wanda yake zaune a Jihar Kauna ya san abinda Gwamnan ya yi na sa ɗansa a makarantar gwamnati kawai wasan barkwanci ne.

“Bari in faɗa muku, mun yi wani gwamna a jihar nan, Balarabe Musa, wanda bai taɓa zama a Gidan Gwamnati ba lokacin da yake kan mulki.

“Ya zauna a gidansa. Na san ‘ya’yan tsohon Gwamna Ahmed Makarfi wannan Capital School ɗin suka yi.

“Na san sauran ‘ya’yan ma’aikatan gwamnati wannan makarantar suke zuwa su ma. To, idan ba wayau ka ke son yi ba, yaudara ko barkwanci, sai ka ƙyale duk ‘ya’yanka su yi makarantar gwamnati.

“Makarantar gwamnati ba tana nufin makarantun firamare ba kawai, akwai makarantun sakandire na gwamnati da jami’o’in gwamnati.

“Ba yanzu ya fara irin wannan diramar ba. Shi ne dai wanda yake zirga-zirga tsakanin hanyar Kaduna zuwa Abuja da kyamarori, yana cewa yana korar masu garkuwa da mutane.

“To, wannan sabon fim ne, a iya sanina, wannan wasan barkwanci ne tunda muna cikin wani zamani a jihar nan na yin amfani da kayayyakin gwamnati, asibitocin gwamnati, yanzu kuma makarantun gwamnati.

“Saboda haka, dai-dai ne ma’aikatan gwamnati, waɗanda aka zaɓa da waɗanda aka naɗa su riƙa yin amfani da banɗakunan haya.

“Wannan shi ne siffa mafi girma na kishin ƙasa da yin aiki na rashin son kai. Ya kamata ka yi amfani da abinda da talakawa ke amfani da shi, wanda shi ne banɗakin haya.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan