Jami’an rundunar ƴan sanda ta ƙasa reshen jihar Kaduna sun bankado wani gida a cikin garin Kaduna da aka tara yara masu ƙananan shekaru da masu matsakaita shekaru, wasunsu kuma daure da mari.
Tun da farko wasu rahotanni sun bayyana cewa an gano wannan gida ne a unguwar Rigasa dake cikin karamar hukumar Igabi, daga cikinsu akwai kananan yara da basu wuce shekaru 10 ba, inda yaran suka tabbatar da cewa ana yin luwadi dasu.
Haka zalika kananan yara sun fallasa cewa ana tilasta musu yin azumi ba a son ransu, amma dai an yi sa’a kwamishinan Yansandan jihar, Ali Janga ya isa wajen, kuma sun dauke da yaran daga gidan, sa’annan zasu kaddamar da bincie.
Wata majiya daga rundunar ƴan sandan tace wasu daga cikin daliban sun taho ne daga kasashen Burkina Faso, Mali da wasu jahohin ƙasashen Afirka.
Jami’an Yan Sanda Sun Gano Wani Gida Da Aka Ɗaure Yara 300 A Kaduna
Turawa Abokai