A ranar Juma’a ne Manajan Daraktan Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA, Baffa Babba Dan’Agundi ya nemi taimakon takwarar hukumar ta Jihar Legas, wato Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas, LASTMA don inganta aikinta a Jihar Kano.
Mista Dan’Agundi ya yi wannan roƙo ne lokacin da ya jagoranci manya-manyan jami’an KAROTA zuwa Hedikwatar LASTMA don yin wata ziyarar aiki ta wuni ɗaya, kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga Olumide Filade, Mataimakin Daraktan Huɗɗa Da Jama’a na LASTMA ya fitar ta bayyana.
Shugaban na KAROTA, wanda ya yaba wa Gwamnatin Jihar Legas bisa ƙoƙarinta na kafa LASTMA, ya kuma yaba da irin rawar da LASTMA ke takawa wajen kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar.
“KAROTA ta zo Legas ne don ta nemi dangantakar aiki bisa yadda za ta inganta aikinta a Jihar Kano, saboda LASTMA ta yi gaba sosai.
“Za a iya ɗaukar dokar zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Legas don inganta aikace-aikacen KAROTA”, in ji Mista Dan’Agundi.
Da yake mayar da jawabi, Mataimakin Janar Manaja na LASTMA, Isaac Adetimiro ya ce jajircewar gwamnatocin da suka gabata a jihar bisa jagorancin jam’iyya ɗaya tun 1999 shi ya taimaka wajen inganta aikin hukumar.
“Wannan hukuma ta zama abar koyi ga sauran hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa na jihohi.
“Za mu ci gaba da yin gwagwarmaya don samun babbar Legas inda ingantacciyar kula da ababen hawa zai inganta harkokin walwala da tattalin arziƙi a jihar”, in ji shi.
Shugaban na LASTMA ya ce Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu yana bada muhimmanci sosai wajen mayar da Legas Wani Birni Dai-dai da Zamani, da kuma Jiha ta Ƙarni na 21 ta hanyar tsarin tattalin arziƙi mai kyau, wanda ingantaccen tsarin kula da zirga-zirgar ababen hawa ke yi wa jagora.
Ya ce Gwamna Olu ya nuna jajircewa ta hanyar sa hannu ga First Executive Order, wata doka dake da manufar kiyaye ambaliyar ruwa, cunkoson ababen hawa da kula da shara a jihar da kuma ziyartar hedikwatar LASTMA a mako ɗaya da rantsar da shi.
Mista Adetimiro ya lissafa wasu ƙalubale da dama da LASTMA ke fuskanta a baya da suka haɗa da dokoki game da yadda take gudanar da aikace-aikacenta, waɗanda hukumar ta riga ta shawo kansu.
Ya ce Dokar Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas da Majalisar Dokokin Jihar Legas ta yi wa kwaskwarima a 2012, ta kuma ƙara yi mata kwaskwarima a 2018 ta samar da ƙa’idoji da kuma haramta zirga-zirgar ga direbobin motocin haya.
Mista Adetimiro ya ce dokar da aka yi wa kwaskwarima ta kuma yi tanadin N20,000 a matsayin mafi ƙarancin tara, ba kamar tsohuwar dokar ba, wadda ta yi tanadin tara mafi yawa ta N50,000.
Ya ce tsohuwar tarar da ba ta taka kara ta karya ba ta sa direbobi suna yi wa dokokin tuƙi hawan ƙawara.
Shugaban na LASTMA ya shawarci KAROTA da ta ɗauki ɗaliban da suka kammala karatun jami’a da yawa aiki kamar yadda ake yi a Legas don su inganta ayyukansu da dangantakarsu da al’umma.
“Waɗannan jami’ai dole a biya su sosai don a hana su cin hanci wanda shi ne babbar cutar dake damun al’ummarmu”, in ji Mista Adetimiro.
Jami’in Huɗɗa da Jama’ar na LASTMA, Olumide Filade, ya ce wakilan na KAROTA sun kuma ziyarci Cibiyar Koyon Tuƙi ta Jihar Legas, LASDRI.
Ya ce ziyarar ta biyo bayan Taron Ƙuli da hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa na jihohi suka yi da Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa, FRSC kwanan nan a Abuja.
Mista Filade ya ce Shugaban FRSC, Boboye Oyeyemi ya ƙarfafa wa sauran jihohi guiwa da su ziyarci Jihar Legas da nufin koyo daga gogewarsu ta aiki.