Dalilan Da Yasa Zaku So Zuwa Taron Kannywood Da Za ayi A Kano

152

A kan gudanar da taruka da yawa amma wasu na shan sahyi ne kawai a watse, sai dai a wannan karon kamfanin Moving Image Limited ya shirya sauya lissafin ta hanyar shirya taron da zai zama shimfida tabarmar farfado da masana’antar Kannywood ta shiga a fara gogayya da ita.

Tabbas babu wanda zai so a bar shi a baya wajen halartar taron musamman ga masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finai, sayarwa, da kuma dillancinsu.

Akwai dalilai da dama da zasu sanya kowa ya so zuwa taron daga ciki akwai:


Karin ilimi
Taron zai gayyato manyan masu ruwa da tsaki a harkar shiryawa da sayarwa tare da dillancin finafinai daga cikin kasar nan da ketare.

Fadada Abokan hulda

Masu iya Magana na cewa kogi bai ki dadi ba, musamman ma a wanann zamani da mutane suke da burika da yawa. Babu wanda zai ki idan har aka bashi damar haduwa da sabbin mutanen da zasu taimaka masa wajen fadada harkallarsa. Tunda taron zai kunshi kwararru daga fannoni da dama kunga kenan akwai damar musayar adireshe da lambar waya domin taimakon juna.

Karbar horo

Ga wadanda suka yi rijista akwai horon da aka shirya bayarwa a fannin shirya fim tun daga tushe da tsakiya yayin daukarsa da kuma bayan an kamala shi. Ga kuma hanyoyin sayar da hajar don samun riba mai nauyi tare da koyar da yadda za a shigar da shi kasuwar duniya.

Samun Kyautuka
Akwai Kyautuka na musamman ga wadanda suka shiga gasar fina-finai da aka sanya.

Domin yin rejista ko neman karin bayani sai a lalube su ta +2348035863023 ko kuma a shiga adireshinsu na yanar gizo https://www.kilaf.org.ng/

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan