Karon Kaho Da Kaho Tsakanin Manchester Da Arsenal Ayau

141

Ayau Litinin kungiyoyin kwallon kafan Manchester United da Arsenal zasuyi karon kaho da kaho a gasar ajin Premier ta kasar Ingila.

Dukkanin kungiyoyin kwallon kafan guda biyu kowacce na fama matsaloli ta rashin nasara tun bayan da manyan masu horas warsu suka barsu wato Sir Alex Peruguson da Arsen Wenger.

Ayanzu wata babbar matsala datake damun kungiyoyin kwallon kafan guda biyu takai ta kawo basa iya halartar gasar zakarun nahiyar turai akowacce shekara.

Awasan da kungiyoyin suka fafata na karshe a tsakaninsu a kakar wasa ta bara Arsenal ce ta doke Manchester United daci 2 da nema.

Ayanzu dai Arsenal nada maki 11 inda Manchester United take da maki 8 daga wasanni 6 da suka fafata daga fara gasar ta Premier ta bana.

Shin ko yaya wasan yau zai kasance ganin kamar hamayyar ta ragu a tsakaninsu idan za a kwatanta lokacin da Captain Roy Kane yake da Captain Viera? Shin ko hamayyar zata wuce tada ganin cewar anshiga wani sabon zamani a duniyar kwallon kafa?.

Ayau din dai Manchester United zasu karbi bakuncin Arsenal inda za a fafata wannan wasa a filin wasa na Oldtraford.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan