Mafi Ƙarancin Albashi: Ƙungiyar Ƙwadago Na Dab Da Tsunduma Yajin Aiki

193

A ranar Laraba ne Haɗaɗdiyar Ƙwangiyar Ƙwadago ta yi barazanar fara yajin aikin ƙasa gaba ɗaya daga ranar 16 ga Oktoba idan Gwamnatin Tarayya ta ƙi yadda a ci gaba da tattaunawa da kwamitin tattaunawa don duba yadda za a tabbatar da ƙarin mafi ƙarancin albashi.

A wani taron ganawa da Hukumar Sasantawa Tsakanin Ma’aikatan Gwamnati ta Ƙasa, JNPSNC a Abuja, NLC da takwararta ta ‘Yan Kasuwa, TUC, sun yi gargaɗin cewa Ƙungiyoyin Ƙwadagon ba za su yi wata-wata ba wajen tsunduma yajin aiki idan gwamnati ta ƙi biya musu buƙatunsu.

A cewarsu, an daɗe ana harziƙa ma’aikatan gwamnati a Najeriya, biyo bayan gazawar Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Ƙwadago na cimma wata matsaya bisa sabon mafi ƙarancin albashi wanda aka amince da shi watanni shida da suka kamata.

A wata sanarwa da Shugaban NLC, Ayuba Wabba da takwaransa na TUC, Quadri Olaleye da Muƙaddashin Shugaban JNPSNC (Tsagin Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa) suka sanya wa hannu, ƙungiyoyin sun ce Ƙungiyar Ƙwadago ta nuna dattaku da haƙuri da gwamnati.

Sun lura da cewa dole Ƙungiyoyin Ƙwadago sun sassauta matsayinsu na farko na samun ƙarin kaso 66.6 cikin ɗari na ƙarin albashin ma’aikatan dake mataki na 07 zuwa 17, ta hanyar karɓar karin kaso 29 cikin ɗari ga ma’aikatan dake matakin 07 zuwa 14, da kuma kaso 24 cikin ɗari ga ma’aikatan dake matakin albashi na 15 zuwa 17.

“Duk da wannan kishin ƙasa, gwamnati ta nace kan cewa za ta iya biyan kaso 11 cikin ɗari ne kawai ga ma’aikatan dake matakin albashi na 07 zuwa 14, da kuma kaso 6.5 cikin ɗari ga ma’aikatan dake matakin albashi na 15 zuwa 17”, in ji sanarwar.

A ta bakinsu, Naira ta rasa darajarta daga ₦150 kan Dalar Amurka Ɗaya ($1) a 2011, zuwa ₦360 kan Dalar Amurka Ɗaya ($1) a 2019, ragin kaso 140 cikin ɗari.

Ƙungiyoyi suka ce tunda aka fara bada mafi ƙarancin albashi na ƙarshe na ₦18,000, ma’aikata ke fuskantar wahalar hauhawar farashi, da kuma tashin goron zabi na farashin kayayyaki da harkokin yau da kullum.

Sun yi nuni da cewa man fetur ya tashi daga ₦87 kowace lita zuwa ₦145 kowace lita wanda ke nufin ƙarin kashi 60 na farashi, kuma an ƙara kuɗin wutar lantarki da kaso 60 cikin ɗari.

“Kwanan nan, an ƙara Harajin Kayayyaki, VAT, daga kaso 5 cikin ɗari zuwa kaso 7.2 cikin ɗari”, in ji sanarwar.

Halin ko-in-kula na ɓangaren tattaunawa na gwamnati ya nuna ya sa da tattaunawar ƙarin albashin ta lalace.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Tayin da gwamnati ta yi na ƙarin albashi da kaso 11 cikin ɗari ga ma’aikatan dake matakin albashi na 07 zuwa 14, da kuma kaso 6.5 ga ma’aikatan dake kan matakin albashi na 15 zuwa 17 ba zai samu karɓuwa ba ga ma’aikatan Najeriya.

“Muna ganin wannan matsayi na gwamnati a matsayin nuna rashin damuwa ga matsalar ma’aikata, kuma yunƙuri ne da gwamnati za ta karɓa da hannun hagu, abinda ta bayar da hannun dama.

“Muna buƙatar a cikin mako ɗaya a dawo da tattaunawar kwamitin dake tattauna ƙarin albashi don kammala aikin da aka fara tun 28 ga Mayu”.

“Shiga yarjejeniya da Ƙungiyar Ƙwadago don tabbatar da albashin ma’aikata dake kan matakin albashi na 07 zuwa 14, ya kamata a ƙara shi da kaso 29 cikin ɗari, na ma’aikatan dake kan matakin albashi na 15 zuwa 17 kuma a ƙara shi da kaso 24 cikin ɗari.

“Muna buƙatar a aiwatar da yarjejeniyar da aka sanya wa hannu ta ƙara albashin ma’aikata daga 18 ga Afrilu, lokacin da aka sanya wa dokar mafi ƙarancin albashi hannu”, in ji su.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa a ranar 18 ga Afrilu ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa dokar sabon mafi ƙarancin albashi hannu.
Amma, tun lokacin a ke ci gaba da tattaunawa kan yadda za a aiwatar da biyan sabon mafi ƙarancin albashin na ₦30,000.

A ranar 14 ga Mayu, Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin da zai tabbatar da biyan sabon mafi ƙarancin albashi, shi ma ya kafa wani ƙaramin kwamitin a ƙarƙashinsa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan