Wasan Najeriya Da Brazil Zai Fuskanci Barazana

200

Akwai yiwuwar wasan Brazil da Najeriya na sada zumunta daza ayi a Singapore ya fuskanci barazana a ranar.

Barazanar kuwa itace ta yanayi inda masu hasashen yanayi sukayi ittifakin za a sami ruwan sama mai karfin gaske aranar 13 ga watan Oktoba a kasar ta Singapore.

Inda aka kara bayyana cewar za ayi ruwa mai karfin gaske ma’aunin yanayi na 30 degree celsius ayankin na Asia inda ruwan zai taba filin wasan na Singapore.

Inda aka bayyana cewar za a buga wasan da misalin karfe 3:00 na safe agogon kasar ta Singapore wanda yayi daidai da karfe 8:00 na dare agogon Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan