Katsina United Da Jigawa Golden Stars Ayau Litinin

126

Ayau Litinin za ayi karon kaho da kaho tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Katsina United da Jigawa Golden Stars awasan share fage na gasar Dr. Ahlan Pre Season Tournament.

Katsina United dai sunyi gyara sosai awannan sabuwar kakar wasan daza a shiga ta NPFL ta 2019 zuwa 2020 musamman wajen sauyin mai horas wa da sukai da kuma sabon shugaban kungiyar da suka nada wato Prince Abdussamad Badamasi da kuma manyan ‘yan wasa da suka saya ciki harda Gambo Mohammed tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Tuni kungiyar kwallon kafan ta Katsina United suke anan Kano inda ake sa ran isowar shugaban kungiyar kwallon kafan ta Katsina ayau wato Prince Abdussamad Badamasi.

Itakuwa kungiyar kwallon kafa ta Jigawa Golden Stars tasami damar haurowa gasar awannan shekarar bayan data ahafe shekaru bata buga gasar ta ajin Premier.

Shin ko wacce irin bajinta kowacce kungiyar kwallon kafa zata taka awannan gasa a tsakaninsu?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan