A ranar Talata ne Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC, ta sake gurfanar da Abdullahi Babalele, wanda ake cewa surukin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ne bisa tuhume-tuhumen badaƙalar kuɗi.
EFCC tana zargin Mista Babalele ne da yin badaƙalar Dalar Amurka $140,000 gab da zaɓukan 2019.
An fara gurfanar da wanda ake zargin ne ranar 14 ga Agusta a gaban Mai Shari’a Nicholas Oweibo, lokacin da kotun ke hutu, inda Mai Shari’a Oweibon ya zauna a matsayin alƙali mai aiki lokacin hutu.
Surukin na Atiku ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa, an kuma bada belinsa a kan kuɗi Naira Miliyan N20, tare da kawo mutum ɗaya da zai tsaya masa.
Amma biyo bayan mayar da ƙarar ga sabon alƙali, Mai Shari’a Cjukwujekwu Aneke, sai aka sake gurfanar da wanda ake ƙara ranar Talatar nan.
A wannan kotun ta biyu ma ya musanta tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Mai Shari’a Aneke ya amince da buƙatar Mista Babalele na ci gaba da cin moriyar sharaɗin belin da Mai Shari’a Oweibo ya ba shi tun da farko.
Bayan an sake gurfanar da shi, sai Mista Babalele ya roƙi kotun da ta ba shi fasfo ɗinsa na tafiye-tafiye don ba shi dama ya je a duba lafiyarsa.
Amma lauya mai gabatar da ƙara, Rotimi Oyedepo, wanda ya bayyana tare da A.O Mohammed, ya soki wannan buƙata, yana mai cewa babu wata alama da ke nuna cewa ba za a iya duba lafiyarsa a Najeriya ba.
Mai Shari’a Aneke ya ɗaga zaman kotun zuwa 11 ga Oktoba don yanke hukunci game da yiwuwar bayar da beli.
A ƙarar, EFCC tana zargin wanda ake ƙara da sa wani Mohammed ya biya zunzurutun kuɗi har Dalar Amurka $140,000 ba tare da zuwa wata cibiyar hada-hadar kuɗi ba.
[…] Muƙalar Da Ta GabataEFCC Ta Ƙara Gurfanar Da Surukin Atiku A Gaban Kotu […]