Sai An Inganta Masana’antu Sannan Tattalin Arzikin Ƙasar Nan Zai Gyaru – Dangote

126

Fitattun masana tattalin arziki da manyan ƴan kasuwa da manyan ma’aikatan banki sun fara wani yunƙurin haɗa hannu wajen bai wa gwamnatin tarayya gamsassun shawarwari akan yadda za’a magance ƙalubalen da tattalin arzikin ƙasar nan ke fuskanta.
Yayin babban taron tattalin arzikin ƙasar nan karo na 25 da ya gudana a Abuja, Aliko Dangote fitaccen attajirin nahiyar Afrika, ya ce ɓangaren masana’antu a ƙasar nan na tallafawa ne da kashi 9 kacal cikin dari maimakon akalla kashi 30 da ya kamata ace ɓangaren na samarwa tattalin arzikin kasar nan.
Aliko Dangote ya ce matuƙar za’a bunƙasa ɓangaren masana’antu a kuma gyara hanyoyin sufuri musamman ɓangaren jiragen ƙasa baya ga faɗaɗa tashoshin ruwan ƙasar nan domin sauƙaƙa hanyar fita da kuma shigo da halastattun kayaki babu shakka zai taimaka matuƙa.
Sai dai Dangote ya ce duk da haka dole ne a magance matsalar fasaƙwauri wadda ke yiwa tattalin arzikin ƙasar nan zagon ƙasa tare kuma da bunƙasa ɓangaren iskar gas da kuma samar da gyara a bangaren musayar kuɗaɗe..

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan