Sadiya Farouq, Ministar Ayyukan Jin Ƙai, Kare Afkuwar Annoba Da Walwalar Jama’a, tana birnin New York na Amurka, don haɓɓaka wani kamfe na Majalisar Ɗinkin Duniya Na Yaƙi Da Talauci yayinda ake ci gaba da jita-jitar cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai aure ta, in ji jaridar The Cable.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter, ministar, wadda ake jita-jitar yau Juma’a za a ɗaura auren ta, ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su shigo a dama da su wajen yaƙi da talauci.
‘Yan Najeriya masu amfani da shafin na Twitter sun tambayi ministar da ta yi bayanin kan auren da ake zargin za ta yi.
Adewale, wani mai amfani da shafin Twitter, ya roƙi ministar da ta wallafa rahotunan da aka ɗauka kafin aure da kuma hotunan wuraren da aka yi hotunan.
“Mai Girma Uwar Gidan Shugaban Ƙasa mai jiran gado, ya kamata mu ga hotunan da aka ɗauka kafin ɗaurin aure da wurin da aka ɗauke su. Bai kamata ke da baba ku kunyata mu ba. ‘Yan adawa ba za su bar mu mu huta ba”, ya rubuta haka a shafin nasa na Twitter.
Wani mai amfani da shafin na Twitter shi ma ya ce ya ce: “Ba yau ne ya kamata a ce ranar ɗaurin aurenki ba? Shiga ciki ki yi kwalliya, ki sa mayafi. Kar ki ɓata ranar baba fa. Ina roƙon ki”.