Kwamishinonin Da Ganduje Zai Ƙara Tafiya Da Su A Wa’adin Mulki Na Biyu

208

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abudullahi Umar Ganduje ya shirya tsaf don naɗa kwamishinoni da zai aiki da su a wa’adin mulkinsa na biyu.

Gwamna Ganduje zai ƙara tafiya da wasu tsofaffin kwamishinoninsa.

Wata majiya a Fadar Gwamnatin Kano ta labarta wa jaridar Daily Trust cewa daga cikin kwamishinonin da su dawo da akwai na Yaɗa Labarai, Malam Muhammad Garba; na Ƙananan Hukumomi, Murtala Sule Garo; na Raya Karkara, Musa Iliyasu Kwankwaso da na Lafiya, Dakta Kabir Ibrahim Getso.

Sauran sun haɗa da Kwamishinan Shari’a, Ibrhim Mukhtar; na Kasuwanci, Ahmed Rabi’u da na Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare, Alhaji Shehu Na’Allah.

A cewar wannan majiya, tuni gwamnan ya aika da sunayen waɗannan kwamishinoni zuwa ga Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa, NDLEA don tantancewa.

“A zahirin gaskiya, waɗanda aka miƙa sunayen nasu sun tsallake tantancewa ta tushe. Ana sa ran fara tantance su ɗaya bayan ɗaya gobe (yau Litinin), kuma za a gama ranar Laraba”, in ji majiyar.

To, amma lokacin da aka tuntuɓe shi don yin ƙarin haske, Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna, Abba Anwar, ya ce ba shi da masaniya game da waɗannan jerin sunayen kwamishinoni.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan