Wani Uba Ya Yi Wa Ƴaƴansa Huɗu Fyade A Jihar Legas

166

Wani mutum mai suna Bassey Archibong, wanda ya ke zaune a gida mai lamba 10 da ke kan titin Kunle Dipo a yankin Majidun Owutu cikin garin Ikorodu ta Jihar Legas, ya gurfana a gaban kotu, bisa laifin yi wa ‘ya’yansa guda hudu fyade, wadanda shekarunsu bai wuce 12 ba zuwa 20.

An bayyana cewa, Archibong ya fara yi wa ‘ya’yansa fyade ne tun a shekarar 2016. An dai gurfanar da Archibong ne a gaban kotun Ikorodu ta Jihar Legas, bisa tuhumar sa da laifuka guda uku, wadanda su ka hada da lalata da ‘ya’yansa da rashin mutunta doka da kuma bata rayuwar ‘ya’yansa.

Sai dai wanda a ke tuhumar ya musanta dukkan laifukan da a ke zargin sa da shi.

Lauya mai gabatar da kara, John Iberedem, ya bayyana cewa, Archibong ya na amfani da abinci wajen sa musa kayan maye, domin ya dauke hankalinsu wajen cimma burinsa na yin lalata da su. Iberedem ya kara da cewa, duk lokacin da zai yi amfani da su sai su ki yarda, inda su ke tunatar da shi cewa, Allah ya hana kuma ya yi alkawarin hukunta duk wanda ya ke aikata wannan lamari.

Lauyan ya cigaba da cewa, wannan laifi ne wanda ya ke da hukuncin a sashe na 265 (2) na dokar manyen laifuka ta Jihar Legas ta shekarar 2019.

Ya ce, “yaran su na wahala a duk lokacin da ya ke kwanciya da su. “Ya na mai bayyana musa cewa, abu komi idan mahaifi ya kwanta da yaransa a wajen Allah. “Ya bayyana wa yaran cewa, Allah ba zai hukunta duk wanda ya kwanta da yaransa.”

An dai karanata hukuncin kamar haka, “kai Bassey Archibong, a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2019, a gida mai lamba 10 kan titin Kunle Dipo da ke yankin Majidun Owuta cikin garin Ikorodu ta Jihar Legas, ka yi lalata da yaranka guda hudu wadanda shekarunsu bai wuce 12 zuwa 20 ba, domin haka ka aikata laifi wanda ya ke da hukunci a sashe na 265 (2) na dokar manyen laifuka ta Jihar Legas ta shekarar 2015.

“Kai Bassey Archibong, a wannan rana da lokaci sannan kuma a gundumar, ka yi lalata da diyarka mai shekara 20 ba tare da izinin ta ba, domin haka ka aikata laifi wanda ya ke da hukunci a sashe na 260 (1) na dokar manyen laifuka ta Jihar Legas ta shekarar 2015.”

Alkali mai shari’a Misis F. A. Azeez, ta bayar da umurnin a cigaba da tsare wanda a ke tuhuma a gidan yari har sai an samu shawarwari daga ma’aikatar shari’a ta jihar. Sannan ta dage sauraron wannan kara har sai ranar 30 ga watan Oktobar shekarar 2019.

Rahoton Jaridar Leadership Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan