Hukumar Kwastam Ta Haramta Shigowa Ko Fitar Da Kaya Ta Iyakokin Tudu

132

Gwamnatin tarayyar ƙasar nan ta sanar da haramta shigowa ko fitar da kaya a iyakokin ƙasar nan da ke kan tudu har zuwa lokacin da aka samu cikakken hadin kai daga sauran ƙasashen da ake makwabtaka da su.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, an fara taron da sauran kasahen makwabtan ne tun a ranar 20 ga watan Agusta 2019 wanda ya hada Hukumar da ke yaki da fasa-kwauri (Kwastam) Hukumar shige da fice ta ƙasa tare da hadin gwiwar rundunar sojoji da wasu hukumomin tsaro.

Shugaban Hukumar Kwastam Kanar Hamid Ali mai ritaya, ne bayyanawa manema labarai hakan yau Litinin inda ya ce zurgazigar kayayyaki daban suke da na mutane a iyakokin ƙasar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan