Jaddawalin Gasar NPFL Ta Kasarnan Daza a Fara

204

Hukumar dake shirya gasar ajin Premier ta kasar nan wato League Management Company ta fitar da jaddawalin yadda za a fara fafata gasar NPFL ta bana.

An bayyana cewar za a fara gasar aranar 27 ga watan Oktoba na 2019 wato sabuwar kakar wasan 2019 zuwa 2020.

Idan ba a manta ba a kakar wasan data gabata kungiyar kwallon kafa ta Enyimba ce ta lashe gasar karkashin mai horas wa Usman Abdallah.

Ga yadda aka fitar da jaddawalin a ranar farko:

Plateau United da Lobi Stars.

Warri Wolves da Akwa United.

Kano Pillars da Rivers United.

Enugu Rangers da Sunshine Stars.

Abia Warriors d da Katsina United.

Ifeanyiubah da Adamawa
United.

Wikki Tourist da Jigawa Stars.

Delta Force da Akwa Starlet.

Heartland da M Mountain Of Fire Ministry.

Enyimba da Nasarawa United.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan