A cewar Majalisar Dinkin Duniya, yanzu haka akwai mutane kimamin miliyan 820 da ke fama da yunwa ko kuma rashin abinci mai gina jiki a sassan duniya.
Hukumar FAO ta bukaci jama’a da su rika cin abinci mai gina jiki da suka hada da ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki tare da kaurace wa na’ukan cimaka masu haifar da teɓa.
Hukumar ta FAO ta ce, mutane na fama da kibar da ta wuce kima saboda dabi’arsu ta kaurace wa na’ukan abincin gona masu gina jiki, inda suka rungumi abinci mai kitse da sikari da gishiri, sannan kuma suke yawan cin naman shanu.
Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa, akwai mutane miliyan 670 da ke fama kibar da ta wuce kima baya ga kananan yara miliyan 160 da su ma ke fama da irin matsalar saboda rashin daidaiton cimaka.
FAO ta bayyana cewa, dungulewar duniya wuri guda, da gina manyan birane da kuma habbakar kudaden shiga, su ne ummul-haba’isin kasalar da ke hana mutane ware lokacin girki a gida, in da a maimakon haka suke sayen abincin da ke illa ga lafiyarsu a manyan shaguna.
A ɓangare guda, Hukumar ta ce, al’ummar duniya na fuskantar matsalar karancin abinci, abin da ke hana su samun isassun abinci masu kara lafiya ga jiki.
Kwararru a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa, rashin abinci mai gina jiki na haifar da cututtuka da dama ga bil’adama, kuma akwai bukatar hada karfi da karfe wajen magance wannan matsalar a cewar FAO.