An Gurfanar Da ‘Yan KAROTA A Kotu Bisa Laifin Siyar Da Takardun Ɗaukar Aiki Na Bogi

45

An gurfanar da jami’an Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA su uku a gaban Mai Shari’a O. A Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya ta Kano bisa laifin siyar da takardun ɗaukar aiki na bogi.

Jami’an su ne Nazifi Ali Cigari, Abbas Tijjani da Ado Aminu.

Dukkaninsu sun amsa laifinsu.

Duba da amsa laifin nasu, sai lauya mai gabatar da ƙara, Musa Isah ya jagoranci Ekene Ikpeama, wani jami’in hukumar, don duba gaskiyar batun.

Mista Ikpeama ya bayyana cewa waɗanda ake ƙarar sun haɗa baki ne da wani, Abduljalal Salisu, wanda ke ƙulla yadda za a damfari jama’a ta hanyar siyar musu da takardun ɗaukar aiki na bogi na Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa, FIRS da na KAROTA.

Shaidar ya ce lokacin da ya samu wani rahoton sirri, sai shi da ‘yan tawagarsa suka yi dirar mikiya a wajen da ake aikata wannan mummunan laifi inda aka kama Mista Abduljalal yana siyar da takardar ɗaukar aiki ga ɗaya daga cikin waɗanda ya damfara.

“Lokacin da na samu rahoton sirrin, sai ni da ‘yan tawagata muka shiga aiki, muka yi dirar mikiya a inda ake aikata laifin wanda yake a wajen shaƙatawa na Fine Time Park da yake ƙaramar hukumar Nasarawa. Da muka je wurin, sai muka samu wani mutum da ake cewa Abduljalal Salihu”, in ji shi.

Mista Ikpeama ya ƙara da cewa wanda ake ƙara na farko shi ma sun gan shi a wajen da ake aikata laifin, amma sai ya ranta a na kare lokacin da ya ga jami’an.

Lokacin da aka kawo Mista Abduljalal Ofishin Shiyya na Hukumar na Kano, ya bayyana cewa ya nemi haɗin kan sauran mutanen uku ne don su nemo masa masu neman aiki, sun kuma sani sarai cewa takardun ɗaukar aikin da yake siyarwa na bogi ne.

Dukkanin waɗanda ake ƙarar sun amsa cewa sun haɗa baki wajen aikata wannan damfara.

A yayin wani bincike da aka yi a motarsu, an samu takardun ɗaukar aiki na FIRS da na KAROTA, takardun da hukumomin biyu suka tabbatar na bogi ne.

Bayan nazarin hujjojin wannan ƙara, Mai Shari’a Egwuatu ya ɗaga ƙarar zuwa 7 ga Nuwamba domin tabbatar da laifin da kuma yanke hukunci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan